Brandon Kendhammer and Wyatt Chandler
|

LPBI Takardar Bayani | Fahimtar “Gida” a Shirin Samar da Zaman Lafiya

Abstract

Samar da zaman lafiya fage ne da ke samun ci gaba a tsakanin al’ummomin da ke fama da tashe-tashen hankula a yankin Kudancin Afirka, sannan ya kasance ɓangare mai muhimmanci na shirye-shiryen masu ba da tallafi na ƙasashen waje da dama. Wannan bunƙasa ya zo da ruɗani game da yadda tsarin shirye-shiryen samar da zaman lafiya suke da kuma yadda za a auna su, sannan ya zo da waɗansu sababbin ɓangarorin da aka yi matsaya game da su. Kai tsaye, duk waɗansu ma’aikata da ke kowane matakin shirin samar da zaman lafiya yanzu sun fahimci muhimmancin shirye-shiryen da suka shafi magance musabbabin tashe-tashen hankula daga tushe da nau’ukansu tare da ƙarfafa mutane da ƙungiyoyi domin bin matakan gargajiya na samar da zaman lafiya “waɗanda ba su tauye haƙƙin ‘yan adam ba” waɗanda suke mayar da hankali kan dabarar shawo kan matsala daga sama domin samun zaman lafiya.

Domin ƙarin bayani, a duba: Kendhammer, Brandon, da Wyatt Chandler. Fahimtar “Gida” a Shirin Samar da Zaman Lafiya. RESOLVE Network, 2021.