LPBI Takardar Bincike | Makiyaya da Zaman Lafiya na Yau da Kullum: Muhimman Hanyoyi da Darussan Wanzar da Zaman Lafiya da Yayyafawa Rikici Ruwa Daga Turkana ta Arewa ta Ƙasar Kenya
Abstract
Wannan takarda na ɗauke da sakamakon binciken da ƙungiyar RESOLVE ta gabatar, « na Makiyaya da Zaman Lafiya Na Yau da Kullum: Muhimman Hanyoyi da Darassu Domin Wanzar da Zaman Lafiya da Yayyafawa Rikici Ruwa daga Turkana ta Arewa a ƙasar Kenya,» daga Caleb Maikuma Wafula. An shafe shekara ashirin, ana tattaunawa da yin muhawara a duk faɗin duniya kan cewa yana tsarin makiyaya da al’asunsu da yanayin tattalin arzikinsu shi ne musabbabin yaduwar rikice-rikice a faɗin yankin Afirika. Makiyaya suna fuskantar matsin tattalin arziki, da muhalli, da zamantakewa da siyasa. A sakamakon haka, yan siyasa da jami’an tsaro suke ɗauka makiyaya a matsayin masu tayar da ƙayar baya, masu barazana ga zaman lafiya da doka a wuaren da suke zaune. Wannan abun ne da ke zahiri kuma ya sa an manta da irin gudummuwa da makiyaya ke bayarwa wajen tabbatar da cigaba mai ɗorewa, da rawar da al’ummar makiyaya ke takawa a yankunansu wajen wanzar da zaman lafiya da tabbatar da cigaba a karkara da alƙaryu da ƙasa baki ɗaya. Wannan sakamakon bincike da aka yi amfani da dabarun bincike mabambanta, binciken ya gano hanyoyi da dabarun gargajiya na wanzar da zaman lafiya da yayyafawa rikici ruwa a al’ummar makiyaya mazauna yankunan Turkana a ƙasar Kenya tare da matsaloli da ƙalubalen da suke fuskanta. Darussan da suke ƙunshe cikin wannan binciken za su taimaka mana wajen fahimtar yadda hukumomi da masana za su iya tunkara da magance matsalar tsaro ta la’akari da wasu buƙatun makiyaya na musamman da kuma zaman lafiya na yau da kullum, musamman ma a yankunan da suke fama da tashe-tashe hankula da masu tsattsauran ra’ayi a yankunan makiyayan.